Iran Ta Yi Allah-Wadai da Kyautar Dala Miliyan 20 da Amurka Ta Ƙayyade Kan Bayanan Sirri game da Shirin Nukiliyarta.

Iran Ta Yi Allah-Wadai da Kyautar Dala Miliyan 20 da Amurka Ta Ƙayyade Kan Bayanan Sirri game da Shirin Nukiliyarta.

Gwamnatin Iran ta yi kakkausar suka ga matakin da Amurka ta ɗauka na bayar da tukuicin dala miliyan 20 ga duk wanda ya samar da bayanan sirri game da shirin nukiliyar ƙasar, inda ta bayyana matakin a matsayin abin ƙyama da takaici.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), Kwamitin Tsaro da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) su fito fili su yi Allah-wadai da matakin Amurka.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne rundunar sojin Amurka ta sanar da bayar da tukuicin har dala miliyan 20, tare da yiwuwar taimaka wa masu bayar da bayanan su ƙaura zuwa wani wuri domin tsira.

Amurka ta ce tana neman bayanai masu muhimmanci kan cibiyoyin nukiliyar Iran, kayan aikin da ake amfani da su da kuma mutanen da ke da alaƙa da shirin.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugabannin hukumomin ƙasa da ƙasa guda uku, Araghchi ya buƙace su da su yi tir da wannan mataki ba tare da wata-wata ba.

Ya kuma sake jaddada matsayar Iran cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne, ba wai domin ƙera makaman nukiliya ba.

A nasa ɓangaren, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha bayyana cewa hare-haren sojin Amurka da aka kai kan muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran a lokacin yaƙin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila a watan Yunin 2025 sun lalata yawancin ƙarfin shirin nukiliyar ƙasar.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin girman barnar da hare-haren suka haddasa ba.

Tun bayan wannan yaƙi, Iran ta hana masu binciken Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya shiga wasu cibiyoyinta da aka kai wa hari, ciki har da Fordow, Natanz da Isfahan.

Rikicin ya ƙara tsananta a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila suka yi sanadin mutuwar Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya ƙara rura wutar faɗa tsakanin ɓangarorin.

A yayin sabon zagayen hare-haren, Amurka da Isra'ila sun sake kai farmaki kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran, duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken girman barnar da aka yi ba.

A halin da ake ciki, ƙasashen Qatar da Pakistan na ƙoƙarin shiga tsakani domin ganin an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai Iran ta dage cewa dole ne Amurka ta cika wasu buƙatunta kafin a sake buɗe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar makamashi a duniya.

Daga cikin buƙatun Iran akwai sakin kadarorinta da Amurka ta ƙwace ko ta daskarar, tare da ɗage takunkuman tattalin arziƙin da aka kakaba mata.

Araghchi ya kuma bayyana a baya cewa tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran za ta zo ne a wani mataki na gaba na ƙoƙarin diflomasiyya.

Rashin jituwa kan shirin nukiliyar Iran dai ya daɗe yana zama babban sanadin takun-saƙa tsakanin Tehran da Washington.

A shekarar 2018, a lokacin mulkinsa na farko, Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama. Yarjejeniyar ta tanadi takaita ayyukan nukiliyar Iran a madadin sassauta takunkuman tattalin arziƙi da aka kakaba mata.

Ahmad B Sani

Manufarmu ita ce samar da sahihan labarai da muhimman bayanai kan al'amuran yau da kullum cikin harshen Hausa da Turanci, domin wayar da kan al'umma da isar da sahihan bayanai ga duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form