Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Amince da Kwangilar Naira Biliyan 5.5 Domin Kawo Karshen Shekaru 10 na Rashin Wutar Lantarki a Kananan Hukumomi Hudu Dake Jihar.

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Amince da Kwangilar Naira Biliyan 5.5 Domin Kawo Karshen Shekaru 10 na Rashin Wutar Lantarki a Kananan Hukumomi Hudu Dake Jihar.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da bayar da kwangilar Naira biliyan 5.5 domin gyara layin wutar lantarki mai ƙarfin 33kV, a wani mataki na dawo da wutar lantarki a ƙananan hukumomi huɗu da suka shafe kusan shekaru 10 ba tare da samun wutar lantarki ba.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Binji, Tangaza, Gudu da Silame, inda al'ummomin yankunan suka shafe tsawon lokaci suna fama da matsalar rashin wutar lantarki.

Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Fadar Gwamnatin Jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a.

Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na jihar, Dakta Bashir Muhammad Achida, ne ya sanar da wannan mataki yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar ranar Laraba.

Achida ya ce ana sa ran aikin gyaran layin wutar zai inganta samar da lantarki a yankunan, bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma inganta rayuwar al'ummar da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya nuna damuwa kan tsawon lokacin da al'ummomin suka shafe cikin duhu, lamarin da ya sa ya amince da wannan babban aikin domin magance matsalar.

Gwamnati Ta Ware Naira Miliyan 988.9 Domin Gyaran Kwalejin Fasaha ta Binji

A wani ci gaba makamancin haka, gwamnatin jihar ta kuma bayar da kwangilar Naira miliyan 988.9 domin gyara Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Binji.

Kwamishinan ya bayyana cewa makarantar ta samu koma-baya sakamakon lalacewar kayayyakin more rayuwa da gine-ginanta, wanda ya shafi ingancin koyarwa da karatu.

Ya ce makarantar ta kasance ɗaya daga cikin cibiyoyin da suka shahara wajen koyar da sana'o'i da fasahohin hannu, amma rashin kula da kayayyakin aikinta ya raunana ikonta na gudanar da ingantaccen horo.

A cewarsa, aikin gyaran zai dawo da martabar makarantar tare da ƙarfafa mata damar koyar da matasa sana'o'i da ƙwarewar fasaha.

Achida ya ƙara da cewa bunƙasa ilimin sana'o'i na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi, rage zaman kashe wando da kuma haɓaka tattalin arzikin jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa waɗannan ayyuka na daga cikin ƙoƙarinta na inganta ababen more rayuwa, samar da damarmakin tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar al'ummar Sokoto.

Ahmad B Sani

Manufarmu ita ce samar da sahihan labarai da muhimman bayanai kan al'amuran yau da kullum cikin harshen Hausa da Turanci, domin wayar da kan al'umma da isar da sahihan bayanai ga duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form