Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukan da Suka Shafi Hakan (ICPC), na nuna wasu sassan bidiyon kyamarorin CCTV a zaman sauraron ƙarar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wadda ya shigar yana neman diyyar naira biliyan 10 kan zargin take masa haƙƙoƙinsa na asali.
Bidiyon ya ƙunshi hotunan wani lamari da ya faru a harabar ofishin ICPC, inda ake tsare da tsohon gwamnan.
El-Rufai ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026 a kan ICPC, shugabanta da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, yana zargin cewa sun take masa haƙƙoƙinsa na asali.
Daga cikin korafe-korafen da ya gabatar akwai zargin hana shi ganawa da matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, a lokacin da yake tsare.
A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai Shari’a Chigozie Onah ya amince da buƙatar ICPC na nuna wasu sassan bidiyon maimakon a nuna cikakken bidiyon, kamar yadda El-Rufai ya nema.
Alƙalin ya umarci kowanne ɓangare da ya zaɓi sassan bidiyon da yake son a nuna a gaban kotu, inda ya ware wa kowane ɓangare mintuna 20 kacal.
Mai Shari’a Onah ya bayyana cewa kotun ba za ta iya ɓata lokaci wajen kallon cikakken bidiyon ba, wanda aka ce ya ɗauki sama da sa’o’i shida.
Haka kuma, alƙalin ya amince da hujjar lauyan ICPC, Yetunde Mosunmola, cewa nuna cikakken bidiyon a bainar jama’a na iya fallasa wasu bayanai masu muhimmanci da suka shafi tsaron cibiyar hukumar.
Alƙalin ya ƙara da cewa idan akwai buƙatar kallon cikakken bidiyon, to sai an nuna shi a ofishinsa.
Bugu da ƙari, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar El-Rufai na a gurfanar da jami’an ICPC guda biyu da suka gabatar da takardun rantsuwa a cikin shari’ar, domin a yi musu tambayoyi a gaban kotu.
Daga ƙarshe, Mai Shari’a Onah ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 1:00 na rana.
Shari’ar ta ta’allaka ne kan zargin El-Rufai cewa hukumomin da ya shigar ƙara sun take masa haƙƙoƙinsa na asali, musamman dangane da zargin hana shi ganawa da iyalansa a lokacin da yake tsare.
Tags
Labarai
