Jirgin Sojin Najeriya Dauke da Mutane 32 Ya Yi Hatsari a jihar Ondo.

Jirgin Sojin Najeriya Dauke da Mutane 32 Ya Yi Hatsari a jihar Ondo.

Jirgin saman sojin Najeriya dauke da mutane 32 ya yi hatsari a jihar Ondo, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto da neman wadanda ke cikin jirgin.

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Kula da Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce jirgin mai lambar wutsiya NGR 931 yana kan hanyarsa ne daga Benin zuwa Legas domin gudanar da wani aikin yau da kullum, kafin daga bisani aka rasa tuntuba da shi da misalin karfe 9:13 na safe.

Daga bisani an gano tarkacen jirgin a kusa da sansanin sojojin ruwa da ke Igbokoda, jihar Ondo.

A cewar Keyamo, bayanan farko sun nuna cewa mutane 32 ne ke cikin jirgin, wadanda suka hada da fasinjoji 25 da ma'aikatan jirgin 7.

Har yanzu ba a bayyana adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba, yayin da jami'an ceto ke ci gaba da gudanar da aikin neman wadanda ke cikin jirgin.

Ministan ya ce ya tattauna da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, tare da tabbatar da cewa ma'aikatar za ta bayar da cikakken hadin kai da taimako wajen gudanar da aikin ceto.

Ana sa ran hukumomin za su fitar da karin bayani yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bincike kan hatsarin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form