Gwamnatin Italiya ta amince da sabbin tsauraran matakan tsaro da suka hada da daurin shekaru biyar a gidan yari ga masu aikata laifukan tashin hankali yayin zanga-zanga, tare da tarar Yuro 20,000, kwatankwacin dalar Amurka 22,440.
Matakan, wadanda gwamnatin Firaminista Giorgia Meloni ta amince da su, sun biyo bayan barkewar rikici yayin zanga-zangar da aka gudanar a biranen Milan, Bologna da Turin, kan hauhawar farashin kayayyaki, karancin albashi, tsadar haya da kuma rashin ingancin ayyukan more rayuwa.
A wani bangare na sabbin matakan, gwamnati ta amince da tura sojoji 500 zuwa birnin Milan har zuwa karshen shekarar 2026 domin karfafa tsaro a muhimman wurare da kuma sa ido kan wuraren da ake ganin suna da hadari.
Sai dai Shugaban Italiya, Sergio Mattarella, ya nuna adawa da bai wa sojojin karin ikon gudanar da ayyukan 'yan sanda, lamarin da ya sa ba a ba su wannan hurumin ba.
Sabbin Hukunce-Hukuncen da Gwamnati Ta Kafa
A karkashin sabuwar dokar, mutanen da suka shiga zanga-zangar tashin hankali tare da wasu mutane fiye da biyar, ta hanyar amfani da abubuwa masu hadari kamar duwatsu, sanduna da wasan wuta, za su iya fuskantar daurin shekaru biyar a gidan yari da tarar Yuro 20,000.
Haka kuma, gwamnati ta tanadi hukunta iyayen yaran da ba su kai shekarun girma ba idan suka lalata dukiyoyin jama'a ko na gwamnati.
Hukumomi za su iya neman diyya daga kadarorin iyayen ko kuma cire kudin daga tallafin da iyalan ke samu daga gwamnati.
Sabuwar dokar ta kuma bai wa hukumomi damar tsare matasa masu shekaru 14 zuwa 18 ta hanyar matakan gudanarwa, ko da ba su aikata wani laifi ba, idan akwai hujjojin da ke nuna cewa suna iya zama barazana ga tsaro.
Bugu da kari, mutanen da suka yi amfani da kafafen sada zumunta ko wasu hanyoyin intanet wajen shirya kungiyoyin da za su aikata tashin hankali yayin zanga-zanga na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari.
Rikicin ya barke ne bayan dubban mutane sun fito zanga-zanga kan tsadar rayuwa da matsalolin da suka shafi tsarin makarantu.
A birnin Milan, wasu masu zanga-zangar sun fara fasa shaguna, satar kayayyaki, kona kadarori da kuma arangama da jami'an 'yan sanda, duk da cewa zanga-zangar ta fara ne cikin lumana.
Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da motocin watsa ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Italiya, LaPresse, ya ce akalla jami'an 'yan sanda biyu ne suka jikkata, yayin da aka tsare kusan masu zanga-zanga 50, wadanda da dama daga cikinsu matasa ne da ba su kai shekarun girma ba.
An kuma samu rahotannin arangama a Bologna da Turin, inda wasu masu zanga-zangar suka yi amfani da duwatsu da wasan wuta wajen kai hari kan jami'an tsaro tare da kafa shingayen hanya.
Sabbin matakan sun jawo ce-ce-ku-ce, inda kungiyoyin kare hakkin bil'adama da wasu shugabannin siyasa suka bayyana damuwarsu kan yiwuwar cewa tsauraran hukunci ba za su magance tushen matsalar ba.
Gregorio Sorgona, masanin tarihi a Jami'ar Palermo, ya ce karuwar rashin daidaiton tattalin arziki da tabarbarewar yanayin rayuwar matasa na daga cikin abubuwan da ke haddasa rashin gamsuwa a kasar.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta magance matsalolin da ke haifar da tashin hankali, maimakon mayar da hankali kan hukunta masu aikata laifuka kawai.
Alkaluman da Al Jazeera ta ruwaito sun nuna cewa farashin muhimman kayayyaki da ayyuka, ciki har da abinci, makamashi, sufuri da kudaden gudanar da gida, ya karu da kashi 68 cikin 100 a Italiya tsakanin shekarar 2000 da 2025.
A wannan lokaci, matsakaicin albashin ma'aikatan da ke aiki na cikakken lokaci ya ragu da kusan kashi biyar cikin 100.
Haka kuma, hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 8.7 cikin 100 a shekarar 2022, sakamakon tsadar makamashi da ta biyo bayan yakin Rasha da Ukraine.
Magajin garin Genoa, Silvia Salis, ta ce wajibi ne a saurari korafe-korafen matasa, tare da daukar matakan da za su taimaka musu wajen samun ingantacciyar rayuwa.
Ta kuma jaddada cewa shigar da matasa cikin harkokin ci gaban al'umma ya kamata ya kasance cikin hanyoyin magance matsalar.
A nata bangaren, kungiyar Associazione Antigone, wadda ke rajin kare hakkin bil'adama a tsarin gidajen yari, ta yi gargadin cewa yawan kama matasa da tsawaita hukuncin daurin kurkuku na iya kara tsananta cunkoson gidajen yarin kasar.
Kungiyar ta kuma bayyana damuwarta kan halin da yaran da ke rayuwa cikin talauci ke ciki, tana mai cewa gwamnati ba ta samar da isassun matakan magance matsalar ba.
Ana Fargabar Sabbin Matakan Za Su Kara Tsananta Rikicin
Masu sukar sabuwar dokar sun yi gargadin cewa wasu tanade-tanadenta na iya bai wa hukumomi damar tsare mutane da dama bisa dalilai da ba su da cikakken bayani, lamarin da ka iya kara dagula al'amura.
Sai dai gwamnatin Italiya na ganin cewa tsaurara matakan tsaro da hukunta masu aikata laifuka zai taimaka wajen dawo da doka da oda tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Masu sukar matakan kuwa sun jaddada cewa magance talauci, rashin aikin yi, rashin daidaiton tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki na da matukar muhimmanci wajen rage rashin gamsuwa da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa.
Tags
Labarai
