Wata kotu a ƙasar Ecuador ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Lenín Moreno, hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar bayan ta same shi da laifin cin hanci da rashawa a wani shari’a da ta shafi gina babbar tashar samar da wutar lantarki ta ruwa a ƙasar.
Moreno, mai shekaru 73, wanda ya shugabanci Ecuador daga shekarar 2017 zuwa 2021, an kuma hana shi riƙe duk wani mukamin gwamnati har abada.
Shari’ar ta shafi tashar samar da wutar lantarki ta Coca Codo Sinclair. Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa kamfanin Sinohydro na ƙasar China, mallakin gwamnati, ya biya kusan dala miliyan 76.1 a matsayin cin hanci tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018 ta hanyar kwangilolin tuntuba na bogi.
Hukumomi sun ce Moreno da wasu ’yan uwansa da abokan huldar kasuwanci sun kasance cikin wata hanyar cin hanci da rashawa, inda ake zargin an tura kuɗaɗen ta asusun bankuna na ƙasashen waje da kuma kamfanonin bogi a wuraren da ake boye haraji.
Masu gabatar da ƙara sun ce Moreno da wasu makusantan ’yan uwansa sun karɓi sama da dala miliyan ɗaya a lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban ƙasar tsakanin 2007 zuwa 2013.
Sai dai Moreno ya ci gaba da musanta zargin, yana mai cewa ba shi da hannu wajen sanya hannu ko kula da kwangilolin aikin. A yayin shari’ar, ya ce ya kamata bincike ya fi mayar da hankali kan jami’an da suka sanya hannu kan kwangilolin da kuma wadanda ake zargin suna karɓar kuɗaɗen rashawa.
An kuma samu matar Moreno da ’yarsa, da ’yan’uwansa maza biyu da matansu, da laifi, inda aka yanke musu hukuncin shekaru biyu da rabi a gidan yari.
Tsohon jakadan China a Ecuador, Cai Runguo, shi ma an yanke masa hukuncin shekaru biyar a gidan yari.
Tashar Coca Codo Sinclair ta fara aiki a shekarar 2016, amma tun daga lokacin take fuskantar matsalolin fasaha.
Moreno ya dawo Ecuador ne daga ƙasar Paraguay domin fuskantar shari’ar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment