Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu, ciki har da manyan jami’an rundunar sojin Lebanon, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin kasar Lebanon a ranar Asabar, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Rundunar sojin Lebanon ta bayyana cewa wani Birgediya Janar da wani Kyaftin da kuma wani soja sun mutu bayan harin da aka kai wa motar soji a hanyar Khardali zuwa Nabatieh.
Wannan na daga cikin hare-haren da suka fi janyo asarar rayukan jami’an sojin Lebanon tun bayan barkewar sabon rikicin.
Sojojin Isra’ila sun ce harin ya faru ne a yankin da suke kallon matsayin filin yaki, inda suka kara da cewa duk wani zirga-zirga a irin wannan yanki na bukatar hadin kai da sanarwa ga rundunarsu.
Sun kuma ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Shugaban kasar Lebanon, Joseph Aoun, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa babban take hakkin ikon mallakar kasar Lebanon ne da kuma dokokin kasa da kasa. Firaministan kasar, Nawaf Salam, shi ma ya soki harin tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an da suka mutu.
A wani hari na daban, mutane shida fararen hula sun mutu yayin da wasu hudu suka jikkata bayan harin jiragen yakin Isra’ila a kauyen Saksakieh da ke kudancin Lebanon. Haka kuma wani mutum ya mutu a harin jirgin maras matuki da ya kai wa wata mota hari a yankin Deir al-Zahrani.
Wadannan hare-hare sun zo ne duk da kokarin da ake yi na tabbatar da tsagaita bude wuta da aka cimma ta hanyar tattaunawar da Amurka ta shiga tsakani.
A gefe guda kuma, kungiyar Hezbollah ta ce mayakanta sun kai hari kan wani tankin yakin Isra’ila nau’in Merkava kusa da iyakar kasashen biyu ta amfani da jirgin maras matuki, inda ta yi ikirarin cewa harin ya yi nasara.
Rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah na ci gaba da ruruwa duk da yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta da aka sanar a watannin baya. Hukumomin lafiya na Lebanon sun ce dubban mutane ne suka mutu ko suka jikkata tun bayan tsanantar rikicin a watan Maris.
Sabbin hare-haren sun kara nuna cewa har yanzu yankin iyakar Isra’ila da Lebanon na cikin mawuyacin hali, lamarin da ke ci gaba da barazana ga duk wani yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment