‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda Biyu da Fararen Hula Uku a Harin Zamfara.

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda Biyu da Fararen Hula Uku a Harin Zamfara.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da ‘yan sanda biyu da fararen hula uku, a wani hari da suka kai a ƙauyen Yarkatsinan Laka da ke ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afka wa al’ummar yankin ne inda suka buɗe wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar waɗannan mutane.

Lamarin ya ƙara tayar da hankalin jama’a kan ci gaba da matsalar tsaro a jihar Zamfara, wadda ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: