Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ya Rasu a ƙasar Masar.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ya Rasu a ƙasar Masar.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Usman Zuru, ya rasu a jiya Litinin a wani asibiti dake ƙasar Masar  bayan yayi fama da rashin lafiya. 

An tabbatar da rasuwar ne ta hanyar wasu majiyoyin kusa da Gwamnatin Jihar Kebbi. 
Zuru, wanda ya wakilci ƙaramar hukumar Zuru a majalisar, yana ɗaya daga cikin sanannun ‘yan siyasa a jihar. 

Gwamnati da iyalan marigayin za su sanar da cikakken shirin jana’iza da na makoki a nan gaba.

0 $type={blogger}: