Sojoji sun hallaka wani Ɗan bindiga, tare da ceto nutane 19 da aka sace a Abuja.

Sojoji sun hallaka wani Ɗan bindiga, tare da ceto nutane 19 da aka sace a Abuja.

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne tare da kuɓutar da mutane 19 da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a yankin Bwari Area Council na Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Rahotanni sun ce mutanen da aka sace sun fito ne daga yankin Byazhin, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Guards Brigade, Kyaftin Olawuyi Itunuoluwa, ya fitar, ya ce dakarun sun samu sahihan bayanan sirri game da inda ‘yan bindigar suke ɓoye da mutanen da suka sace a yankin Gidan Dogo.

Ya bayyana cewa dakarun sojojin, tare da haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda da kuma ’yan banga na gari, sun kai samame a wurin domin ceto mutanen.

Sanarwar ta ce da isar dakarun, sun yi arangama da ‘yan bindigar wanda ya rikide zuwa musayar wuta. 
A yayin artabun ne aka kashe ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen, yayin da sauran suka tsere cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.

Jami’in ya ƙara da cewa dakarun sun samu nasarar kuɓutar da dukkan mutane 19 da aka sace, inda daga bisani aka kai su wurin da za su samu kulawa.

Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da wata bindiga ƙirar gida daga hannun ‘yan bindigar.

A nasa ɓangaren, kwamandan Guards Brigade, Birgediya Janar Adebisi Onasanya, ya yaba wa dakarun da sauran jami’an tsaro kan jajircewar da suka nuna wajen gudanar da aikin.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙara zage damtse wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka domin tabbatar da tsaro a Abuja da ma kewayenta.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form