Rundunar Sojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da kama wani da ake zargi da safarar makamai, a wasu hare-hare daban-daban da suka gudana a jihohin Filato da Kaduna.
Rahotan ya ce, dakarun Joint Task Force Operation Enduring Peace sun ceto mutanen ne a yankin Kanam na Jihar Filato.
Rahoton ya ce an sace mutanen tun 22 ga watan Fabrairu, 2026 a Æ™auyen Mansur da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi, kafin a cafke masu garkuwar yayin da suke Æ™oÆ™arin kai su maboyar ‘yan bindiga.
Bayan farmakin sojoji, ‘yan bindigar sun tsere suka bar mutanen, inda daga bisani aka yi musu tambayoyi kafin a fara shirye-shiryen mayar da su hannun iyalansu.
A wani samame kuma a Jihar Kaduna, sojoji sun kama wani mutum mai suna Vincent Ibrahim (shekaru 36) a yankin Sanga, bayan da aka same shi da bindigogi guda biyar da aka kera ba bisa ka’ida ba, yana Æ™oÆ™arin kai su zuwa Kafanchan, Inda yake hannun hukuma domin ci gaba da bincike.
Sojojin sun bayyana cewa wadannan nasarori na daga cikin Æ™oÆ™arin da suke yi na murÆ™ushe ayyukan ‘yan bindiga da dillalan makamai, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan da abin ya shafa.
Tags
Labarai
