Duk da Asarar Manyan Shugabanninta, Iran Na Ci Gaba da Tsayawa Tsayin Daka a Yakin da ta ke yi da Israi'la da Amurka.
Tun bayan fara yakin da ke tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila, an kashe ma ƙasar Iran manyan shugabanni da dama, ciki har da tsohon Jagoran Kolin kasar, Ayatollah Ali Khamenei da kuma babban jami’in tsaro Ali Larijani.
Sai dai duk da wannan babbar asara, gwamnatin Iran na ci gaba da tsayawa da kafafunta, ba tare da nuna alamun rugujewa ba.
A farkon kwanakin yakin, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Iran ta shafe kusan shekaru 20 tana nazarin yadda Amurka ke tafiyar da yakokinta, domin gina wata dabarar yaki da ake kira “Mosaic Defense.”
Ya ce wannan tsari na bai wa Iran damar ci gaba da fafatawa ko da babu cikakken shugabanci na tsakiya, domin an tsara tsarin ne ta yadda bangarori daban-daban za su iya gudanar da ayyuka da kansu.
Masana na ganin cewa wannan dabarar ce ke taimakawa Iran wajen jure hare-haren da take fuskanta, tare da ci gaba da yakar abokan gaba duk da asarar manyan shugabanninta.
News Translation in English Language.
Despite Loss of Top Leaders, Iran Remains Resilient in War with Israel and the United States.
Despite the loss of several high-ranking officials, Iran continues to stand firm in its ongoing conflict with Israel and the United States.
Since the outbreak of the war, a number of prominent Iranian figures have reportedly been killed, including former Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei and senior security official Ali Larijani.
However, despite these significant losses, Iran’s government has remained intact, showing no clear signs of collapse.
In the early days of the conflict, Iran’s Foreign Minister, Abbas Araghchi, stated that the country had spent nearly two decades studying how the United States conducts its wars in order to develop a military doctrine known as “Mosaic Defense.”
He explained that this strategy allows Iran to continue fighting even without a fully centralized leadership, as it is designed in a way that enables different units to operate independently.
Analysts believe that this approach has helped Iran withstand ongoing attacks while maintaining its resistance against its adversaries, despite the loss of key leaders.

0 Comments:
Post a Comment