Akalla mutane 31 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar Bam a masallaci a Islamabad, babban birnin ƙasar Fakistan.
Wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin 'yan Shi'a a Islamabad ya kashe akalla mutane 31 tare da raunata wasu da dama, a daya daga cikin hari mafi muni da aka samu a babban birnin Pakistan.
Fashewar bam din mai karfin gaske ya afku ne a masallacin Khadija Tul Kubra da ke yankin Tarlai Kalan na Islamabad a kudu maso gabashin Islamabad, a lokacin sallar Juma'a.
Mataimakin firaministan Pakistan Ishaq Dar ya yi Allah wadai da lamarin da cewa wani harin kunar bakin wake ne na matsorata akan masu ibada da ba su ji ba ba su gani ba.
"Yin kai hari kan wuraren ibada da fararen hula babban laifi ne ga bil'adama da kuma keta ka'idojin Musulunci.
Tun da farko wani babban jami'in 'yan sanda ya shaidawa Aljazeera bisa sharadin sakaya sunansa cewa fashewar da alama harin kunar bakin wake ne amma har yanzu ba a tantance ainihin musabbabin hakan ba.
"Kungiyarmu tana nan a wurin kuma muna kan aiwatar da tabbatar da dalilin," in ji shi.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharin ya tarwatsa kansa ne bayan an tsayar da shi a kofar masallacin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Fakistan ta ce an kai mutane 169 asibiti bayan da jami'an ceto suka isa wurin da fashewar ta afku.
Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwaki masu zubar da jini a kwance a kasan masallacin, kewaye da fashe-fashen gilashi da tarkace.
A asibitin Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya ta Pakistan da 'yan jaridar AFP sun ga manya da yara da yawa ana dauke da su a kan gadajen asibiti wasu babu hannayensu da kafafu.
