Alhaji Abubakar Abdullahi, limamin Yelwa, Gindin Akwati a Barikin Ladi, Plateau, wanda ya yi fice a shekaran 2018 wajen kare mabiya Addinin Kirista daga kisa a rikicin Jos, ya rasu a daren Alhamis bayan fama da rashin lafiya.
Marigayin ya shahara ne a fadin kasar da ma duniya a watan Yunin 2018, lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka afkawa al'umomin Barkin Ladi.
Inda ya bude masallacin sa da gidan sa domin bayar da mafaka ga daruruwan mabiya addinin Kirista, inda rahotanni suka ce ya ceci rayuka kusan 300, kuma ya ki mika su duk da barazanar da aka yi wa rayuwarsa a lokacin.
Ayyukan jarumtakar da ya yi yasa ya sami karɓuwa sosai, gami da lambar yabo ta 'Yancin Addini na Duniya ta 2019 daga gwamnatin Amurka.

0 Comments:
Post a Comment