Jihar Georgia ta kasar Amurka ta baiwa Nnamdi Kanu, shaidar girmamawa na zama dan kasar Amurka

Jihar Georgia ta kasar Amurka ta baiwa Nnamdi Kanu, shaidar girmamawa na zama dan kasar Amurka

Gwamnatin Jihar Georgia ta ƙasar Amurka ta baiwa Shugaban Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, shaidar girmamawa na zama dan kasar Amurka.

Yanzu haka dai Kanu yana zaman gidan yari a gidan yari na Sokoto bayan da aka yanke masa hukuncin ta'addanci da gwamnatin Najeriya ta shigar masa.

Sakataren Jihar Georgia, Brad Raffensperger, ta ayyana Kanu a matsayin ‘Dan kasa mai daraja a jihar Georgia’ a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 16 ga Janairu, 2026.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ya kamata a amince da shugaban kungiyar ta IPOB a matsayin jakadan fatan alheri na Jihar ta Jojiya.

Wani tsohon jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Uche Ajulu ne, ya karbi Lambar karramawar daga hannun Raffensperger
a madadin Nnamdi Kanu a Jojiya, Amurka, ranar Juma'a.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form