Jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Khamenei

Jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Khamenei

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Khamenei, ya ce kasar Iran ba za ta taba mika wuya sakamakon matsin lamba ba, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya bukata, ya kuma bayyana cewa Isra'ila ta yi babban kuskure.

A jawabin nasa da ya yi ta gidan talabijin a yau Laraba, Khamenei ya gargadi Amurka da cewa duk wani harin soji kan Iran zai haifar da "mummunan sakamakon da ba za a iya kwatantawa ba."

Inda yace:
"Masu hikima wadanda suka san Iran da al'ummarta da tarihinta ba su taba yin magana da wannan kasar da harshen barazana ba, domin Iraniyawa ba sa mika wuya ga abokan Gaba".

Khamenei, wanda ke kan karagar mulki tun a shekarar 1989 kuma mai zartar da hukuncin karshe a Iran, ya sha alwashin cewa kasarsa ba za ta nuna tausayi ga mahukuntan Isra'ila ba, sa'o'i bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci Tehran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba.

Tun bayan harin da Israi'la ta kai Iran a daren juma'a Kasashen biyu ke kai ma junansu hare-hare ba kakkautawa, inda Israi'la ta dau alwashin lalata cibiyoyin tashar makamin Nukiliyan Iran yayin da ana ta banaren Iran ta dau alwashin mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa cikin Israi'la.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: