Me Falasdinawa ke nufi da ranar Nakba a tarihinsu?

Me Falasdinawa ke nufi da ranar Nakba a tarihinsu?

Shin kasan me Ranar Nakba ke nufi a wajen Falasdinawa? 

A kowace shekara a ranar 15 ga Mayu, Falasdinawa a duniya suna bikin tunawa da ranar Nakba, wacce ta ke nufin bala'i da hausa, Ranar da Isra'ila ta Kori Falasdinawa daga kasarsu ta haihuwa, Falasdinu a shekaran 1948. 

Bayan samun goyon bayan gwamnatin Birtaniya wajen kafa kasar yahudawa a kasar Falasdinu, a ranar 14 ga watan Mayun shekara ta 1948, Sojojin yahudawan sahyoniya suka ayyana kafa kasar Isra'ila a Kasar falasdinu, Kuma a ranar 15 ga watan Mayun 1948 aka fara fatattakar Falasdinawan daga garuruwansu, lamarin da ya haifar da yakin farko tsakanin Larabawa da Isra'ila. 


A wancan lokacin Sojojin yahudawan sahyoniya sun kori a kalla Palasdinawa 750,000 daga gidajensu da yankunansu tare da kwace kashi 78 cikin 100 na kasar Falasdinu mai tarihi. 

Sauran kashi 22 cikin 100 kawai aka bar ma Falasdinawa Inda aka raba su zuwa yankunan da a yanzu suke mamaye da gabar yammacin kogin Jordan da yankin Zirin Gaza da aka yiwa kawanya.

Tun daga wancan lokacin na shekaran 1948 Al'ummar Falasdinawa ke cikin tashin hankali da cin zarafi daga Kasar Isra'ila wacce turawan yamma ke goyon baya, wacce Kuma a har kullum burinta shine mamaye sauran Yankunan da aka bar ma Falasdinawa su cigaba da zama na Yammacin kogin Jordan da Zirin Gaza.

Article Translation in English Language.

Every year on May 15, Palestinians around the world celebrate Nakba Day, which means disaster in English, the day Israel expelled Palestinians from their homeland, Palestine in 1948. 

After receiving the support of the British government in establishing a Jewish state in Palestine, on May 14, 1948, the Zionist forces declared the establishment of the State of Israel in Palestine, and on May 15, 1948, the Palestinians were expelled from their cities, which led to the first war between the Arabs and Israel.

At that time, the Zionist Army expelled at least 750,000 Palestinians from their homes and areas and seized 78 percent of the historical land of Palestine. 
The remaining 22 percent was left to the Palestinians where they were divided into the areas that now occupy the West Bank of the Jordan River and the besieged Gaza Strip. 

Since that time in 1948, the Palestinian people have been in violence and abuse from the State of Israel, which is supported by the Western nations, and whose goal is to occupy the rest of the territories that the Palestinians have been allowed to continue living in, the West Bank and the Gaza Strip.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: