'Ya'yan attajirin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka, Aliko Dangote, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shirin mahaifinsu na bayar da kashi daya cikin uku na dukiyarsa da aka kiyasta ta kai dala biliyan 36.5 domin ayyukan jin kai da tallafa wa al'umma.
A wata hira da ta yi da Bloomberg, 'yarsa Halima Dangote ta ce iyalan Dangote suna maraba da wannan shiri, wanda zai kai sama da dala biliyan 12 ga ayyukan agaji da ci gaban al'umma.
Idan aka aiwatar da shi, zai kasance cikin manyan gudummawar jin kai da wani attajirin Afirka ya taba sanarwa.
Wannan sanarwar na zuwa ne yayin da Kamfanin Dangote Group ke kara bai wa 'ya'yansa mata uku—Halima da Fatima da Mariya—manyan mukaman jagoranci a sassa daban-daban na kamfanin, a wani bangare na shirin mika ragamar tafiyar da harkokin kasuwancin iyali nan gaba.
Halima na kula da ofisoshin kamfanin da ke Dubai da Landan sai Fatima na jagorantar harkokin kasuwanci a bangaren makamashi, yayin da Mariya ke kula da dabarun kasuwanci a bangaren abinci da siminti.
Aliko Dangote, wanda zai cika shekara 70 a shekara mai zuwa, ya sha bayyana cewa burinsa shi ne ya yi amfani da dukiyarsa wajen samar da sauyi mai dorewa ga rayuwar al'umma.
Ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, wadda aka kafa a shekarar 1994 tare da asusun dala biliyan 1.25, ya tallafa wa shirye-shiryen kiwon lafiya da ilimi da inganta abinci mai gina jiki da agajin gaggawa da yaki da talauci a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Haka kuma, gidauniyar ta yi hadin gwiwa da gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa wajen aiwatar da shirye-shiryen rigakafi da ciyar da dalibai a makarantu da kula da lafiyar mata masu juna biyu da yara, da kuma bayar da agajin gaggawa ga wadanda bala'o'i suka shafa.
Masu sa ido na ganin goyon bayan da 'ya'yan Dangote suka nuna ga wannan shiri alama ce ta hadin kan iyalin wajen tabbatar da sauyin jagoranci cikin kwanciyar hankali, yayin da Dangote Group ke shirin fadada kasuwancinsa da nufin zama kamfani mai darajar dala biliyan 100 nan da karshen wannan shekarun goma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment