Dalilin da Ya Sa Na Zaɓi Kwankwaso a Matsayin Mataimakina – Peter Obi.

Dalilin da Ya Sa Na Zaɓi Kwankwaso a Matsayin Mataimakina – Peter Obi.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A wata hira da ya yi, Obi ya ce sun haɗa kai ne saboda suna da manufa iri ɗaya ta fitar da 'yan Najeriya daga talauci ta hanyar ilimi  da bunƙasa tattalin arziki da kuma inganta jarin ɗan Adam.

Obi ya ce shi da Kwankwaso sun yi imani cewa ilimi ne ginshiƙin canja al'umma da kuma gina Najeriya mai ci gaba.

"Kwankwaso ya yi imani da fitar da mutane daga talauci ta hanyar ilimi, ni ma haka na yi imani. 
Muna da manufa guda ta gina Najeriya ta hanyar zuba jari a cikin al'ummarta," in ji Obi.

Ya kuma musanta rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakaninsa da Kwankwaso, yana mai cewa suna aiki tare cikin haɗin kai domin samar da shugabanci mai kawo sauyi, ba siyasar anfani ta kashin kai ba.

Obi ya ƙara da cewa haɗin kansu ya samo asali ne daga burinsu na samar wa Najeriya makoma mai kyau, yana mai cewa magoya bayan ƙungiyar Obidient Movement da Kwankwasiyya Movement suna da buri iri ɗaya na ganin an sauya ƙasar zuwa alheri.

Da yake magana kan dalilin da ya sa ba su haɗa kai ba a zaɓen 2023, Obi ya ce ya fi mayar da hankali kan makomar Najeriya fiye da abubuwan da suka faru a baya.

Ana sa ran haɗakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso za ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙawancen siyasa da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya na shekarar 2027.

0 $type={blogger}: