Aston Villa ta zama zakarar gasar UEFA Europa League bayan doke SC Freiburg da ci 3-0 a wasan karshe da aka buga ranar Laraba a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Kungiyar ta Premier League ta nuna bajinta a filin wasa na Tupras Stadium, inda Youri Tielemans da Emiliano Buendía da Morgan Rogers suka zura kwallayen da suka tabbatar da nasarar.
Tielemans ne ya fara bude raga a minti na 41 da wata gagarumar bugu daga sama, yayin da Buendía ya kara ta biyu da wata kwallo mai kayatarwa.
Morgan Rogers ya kara ta uku a farkon rabin lokaci bayan karbar kwallo daga Buendía, wanda ya sanya magoya bayan Villa fara murnar nasara tun da wuri.
Wannan nasara ita ce babbar kofin Turai ta farko da Aston Villa ta lashe cikin sama da shekaru 40, sannan kuma kofinta na farko cikin shekaru 30.
Kocin kungiyar, Unai Emery, ya kafa sabon tarihi bayan lashe kofin Europa karo na biyar, mafi yawa a tarihin gasar. Emery ya taba lashe kofin sau uku tare da Sevilla sannan sau daya tare da Villarreal kafin wannan nasarar da Aston Villa.
Da wannan nasara, Aston Villa ta samu gurbin buga UEFA Super Cup inda za ta kara da wanda ya yi nasara tsakanin Arsenal da Paris Saint-Germain a wasan karshe na UEFA Champions League.

0 $type={blogger}:
Post a Comment