Akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu a sabon hare-haren jiragen saman sojin Isra’ila a kudancin Lebanon, a cewar Hukumar Labaran Ƙasar ta Lebanon (NNA), duk da yarjejeniyar tsagaita bude wutan da aka cimma da gwamnatin Lebanon.
Mafi munin harin ya auku ne a ƙauyen Doueir, inda jiragen yaƙin Isra’ila suka kashe mutane biyar tare da jikkata wasu biyu, bayan da gidaje da dama suka rushe.
A wani hari daban, mutane biyu sun mutu kusa da wani asibiti a Tibnin, yayin da wani mutum ya rasu a harin jirgin sama mara matuƙi a Burj Shemali da ke yankin Tyre. Haka kuma, Jami’an agajin gaggawa na Red Cross sun gano gawar wani mutum a kusa da garin Shebaa.
Waɗannan hare-hare sun biyo bayan wasu hare-haren da aka kai kwana ɗaya da ya gabata, inda aka kashe akalla mutane 16 a kudancin Lebanon, ciki har da mata da yara.
Hezbollah ta ce mayakanta sun yi artabu da sojojin Isra’ila a wasu garuruwa da ke kudancin Lebanon, ciki har da Haddatha da Biyyada da Rashaf.
Rahotanni sun kuma nuna cewa sojojin Isra’ila na ci gaba da fadada hare-hare zuwa gabashin Lebanon, musamman yankunan kwarin Bekaa.
A cewar hukumomin Lebanon, tun daga lokacin da rikici ya ƙara tsananta, fiye da mutane 3,000 sun rasa rayukansu, yayin da sama da miliyan 1.6 suka rasa muhallansu.
Wannan sabon tashin hankali na faruwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen cimmawa, wadda aka tsawaita har zuwa farkon watan Yuli.

0 $type={blogger}:
Post a Comment