Rundunar Sojin Iran ta fitar da gargaɗi mai ƙarfi inda ta bayyana cewa tsaron yankin Tekun Fasha da Tekun Oman zai kasance “cikin rashin tabbas”, a yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka kan batun yiwuwar toshe mashigar jiragen ruwan Iran.
A cewar rundunar sojin Iran, duk wani hari ko matakin takaita ayyukan tashoshin jiragen ruwan Iran zai iya haifar da martani mai faɗi a yankin, wanda zai iya sanya dukkan tashoshin jiragen ruwa na yankin cikin rashin tsaro.
Wannan gargadi na zuwa ne bayan rahotannin da ke nuna cewa Amurka na duba yiwuwar ko ta fara taka-tsantsan ko killace hanyoyin jiragen ruwa na Iran, musamman a mashigin Strait of Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci a kasuwancin man fetur na duniya.
Iran ta yi watsi da wannan mataki, tana mai kiransa “fashi da makami”, tare da yin barazanar mayar da martani idan aka matsa mata da karfi a yankin.

0 $type={blogger}:
Post a Comment