Wani Kwamishina a gwamnatin Jihar Kano ya sake yin murabus daga mukaminsa, lamarin da ke nuna ci gaba da sauye-sauye a cikin majalisar zartarwar jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Umar Haruna Doguwa, Kwamishinan Harkokin Ruwa na Jihar Kano, ya mika takardar murabus dinsa, inda ya yanke shawarar ficewa daga mukamin da yake rike da shi.
An bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus din nasa. Duk da haka, ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa kwamishinan ya ajiye aikinsa ba a hukumance.
Wannan murabus na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a cikin majalisar gwamnatin Kano, inda wasu kwamishinoni ma suka bar mukamansu a baya-bayan nan, abin da ke jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar.
Tags
Labarai
