Sojojin Isra’ila Biyu Sun Mutu Sakamakon wani harin Kungiyar Hizbullah a Kudancin Lebanon.

Sojojin Isra’ila Biyu Sun Mutu Sakamakon wani harin Kungiyar Hizbullah a Kudancin Lebanon.

Rundunar Sojin Israi'la IDF ta sanar da mutuwar sojojinta biyu a wani hari da aka kai a kudancin Lebanon, lamarin da ke nuna yadda rikici tsakanin Isra’ila da mayakan Hizbullah ke kara tsananta.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce sojojin sun mutu ne yayin wani farmaki da aka kai kan dakarunta a yankin iyaka da ke kudancin Lebanon. 
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne da makamin roka wanda ya afkawa wata mota ta sojojin Isra’ila.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar hare-hare tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah a yankin iyakar Lebanon, wanda ya kara tayar da hankalin yiwuwar fadada rikicin a Gabas ta Tsakiya.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa wannan sabon lamari na iya kara dagula yanayin tsaro a yankin, musamman a daidai lokacin da rikicin da ke kara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila ke kara jawo hankalin kasashen duniya.

News Translation in English Language.

Two Israeli Soldiers Killed in Southern Lebanon.

The Israel Defense Forces (IDF) has confirmed that two of its soldiers were killed during an attack in southern Lebanon, as tensions continue to escalate along the Israel-Lebanon border.

In a statement released by the military, the IDF said the soldiers were killed when their unit came under attack while operating near the border area in southern Lebanon. Reports indicated that the attack involved a rocket or anti-tank missile that struck an Israeli military vehicle.

The incident comes amid ongoing exchanges of fire between Israeli forces and the Lebanese armed group Hezbollah, raising concerns about a possible escalation of the conflict in the region.

Security analysts warn that the development could further destabilize the Middle East, particularly at a time when tensions between Iran and Israel are already intensifying.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form