Wani babban jami’in rundunar sojojin Najeriya, wanda ke shugabantar wani sansanin soja, ya rasa ransa a yayin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai masu hari a Jihar Borno.
Rahotanni daga wurin da lamarin ya faru sun ce ‘yan ta’addan sun farmaki sansanin ne da manyan makamansu, inda suka yi musayar wuta da sojojin kafin su bindige kwamandan har lahira, tare da jikkata wasu sojoji a yayin harin.
Ana ci gaba da samun tashin hankali a yankin Ngoshe na karamar hukumar Gwoza, inda ‘yan Boko Haram ke riƙe da wasu sassa na garin, kwana kadan bayan sun kai wasu hare‑hare da suka haifar da asarar rai da sace jama’a.
Bugu da ƙari, an ce wasu mutane sama da 300 ne, ciki har da mata da yara, aka sace su a wannan yanki yayin wasu hare‑haren da suka faru a makon jiya, lamarin da ya ƙara jefa yankin cikin zurfin rikici da matsanancin hali ga fararen hula.
Hukumomi daga rundunar sojojin Najeriya da Ƙungiyar Hadin Gwiwar Tsaro ta (Operation HADIN KAI) sun tabbatar da ayyukan daukar mataki domin yakar ‘yan ta’addan, amma har yanzu ‘yan Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai farmaki kan sansanonin soja da al’ummomi fararen hula a arewa maso gabashin Najeriya.
News Translation in English Language.
Boko Haram Attack in Borno Claims Life of Nigerian Military Commander.
A senior officer of the Nigerian Army, who was commanding a military base, has been killed following an attack by Boko Haram insurgents in Borno State.
Reports from the scene indicate that the insurgents stormed the military facility with heavy weapons, engaging soldiers in a fierce gun battle before fatally shooting the commanding officer. Several other soldiers were also injured during the assault.
Tension continues to mount in Ngoshe, a community in Gwoza Local Government Area, where Boko Haram fighters are reportedly holding parts of the town. The development comes just days after a series of attacks in the area that resulted in casualties and the abduction of residents.
In addition, more than 300 people—including women and children—were reportedly abducted in the area during attacks carried out last week, further worsening the security situation and humanitarian conditions for civilians.
Authorities from the Nigerian Armed Forces and the Operation HADIN KAI Joint Task Force say efforts are ongoing to confront the insurgents. However, Boko Haram militants continue to launch attacks on military formations and civilian communities across northeastern Nigeria.
Tags
Labarai
