Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa nasarorin da jami’an tsaro suka samu wajen fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram daga Dajin Sambisa ne ya sa suka koma kai hare-hare a wasu garuruwan jihar.
Zulum ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya kara da cewa bayan an kori ‘yan ta’addan daga dajin, sun kai hari a garin Ngoshe domin huce takaici kan fararen hula.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa tare da jami’an tsaro na ci gaba da ɗaukar matakai domin fatattakar ‘yan ta’adda gaba ɗaya daga sassan jihar.
News Translation in English Language.
Military Success Against Boko Haram Pushing Terrorists to Attack Towns - Zulum.
The Governor of Borno State, Babagana Umara Zulum, has said that recent successes recorded by security forces against Boko Haram in the Sambisa Forest are responsible for the group’s renewed attacks on some communities.
Zulum made the remark during a meeting with journalists, explaining that after militants were pushed out of the forest, they launched an attack on the town of Ngoshe in retaliation, targeting civilians.
The governor stressed that his administration, in collaboration with security agencies, is continuing efforts to completely eliminate terrorist threats from all parts of the state.
Tags
Labarai
