Kamfanin matatar man Dangote ya Kara Farashin Man Fetur Zuwa N1,175 kan kowace Lita.

Kamfanin matatar man Dangote ya Kara Farashin Man Fetur Zuwa N1,175 kan kowace Lita.

Kamfanin matatar man fetur na Dangote ya sanar da kara farashin man fetur zuwa ₦1,175 kan kowace lita, Wannan shine karin farashi na uku cikin mako guda. Inda farashin ya tashi daga ₦774 zuwa ₦995 Sannan yanzu ₦1,175 kan kowace lita.

Haka zalika, kamfanin ya kara farashin Gas Oil (man dizel) zuwa ₦1,620 kowace lita.

Masana sun danganta wannan karin farashi da hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya da kuma wasu matsaloli na rarraba man fetur daga tankuna, wanda ke haifar da karin farashin a matakin matatar man.

Wasu masana harkar mai sun yi kira ga samar da danyen mai mai rahusa domin rage wannan tashin farashi, yayin da ake kiyasin cewa idan matsalolin kasuwar duniya suka ci gaba, farashin man fetur din zai iya karuwa fiye da haka nan gaba.

News Translation in English Language.

Dangote Refinery Increases Petrol Price to ₦1,175 per Litre.

Dangote Refinery has announced an increase in the price of petrol to ₦1,175 per litre, marking the third hike in a single week. The price has risen from ₦774 to ₦995, and now to ₦1,175 per litre.

In addition, the company has raised the price of Gas Oil (diesel) to ₦1,620 per litre.

Experts attribute the price hike to rising crude oil prices in the global market and distribution challenges from storage tanks, which are pushing costs higher at the refinery level.

Some industry specialists are calling for the provision of cheaper crude oil to help ease the price increases. Analysts warn that if global market challenges continue, petrol prices may rise further in the near future.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form