Gwamnan Kano Ya Karɓi Tallafin Buhunan Shinkafa 100,000 Daga Gidauniyar Aliko Dangote.

Gwamnan Kano Ya Karɓi Tallafin Buhunan Shinkafa 100,000 Daga Gidauniyar Aliko Dangote.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 da Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar, domin tallafawa marasa ƙarfi a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano, gwamnan ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa wannan taimako, yana mai cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da ake cikin watan Ramadan, lokacin da buƙatu ke ƙaruwa.

Gwamnan ya jaddada cewa za a raba tallafin cikin gaskiya da adalci ta hannun shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da cewa ya isa ga mutanen da aka nufa.

A nashi bangaren, Kwamishinan Noma da Albarkatun Ƙasa na Jihar Kano, Danjuma Mahmud, ya yaba wa gidauniyar Dangote bisa bai wa gwamnatin jihar damar kula da rabon tallafin kai tsaye, wanda zai rage matsalolin rashin gaskiya a lokacin rarrabawa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form