Fransa Da China Sun Yi alkawarin hada kai don kwantar da tashin hankali tsakanin Iran da Israi'la da Amurka.

Fransa Da China Sun Yi alkawarin hada kai don kwantar da tashin hankali tsakanin Iran da Israi'la da Amurka.

Kasashen Faransa da China sun bayyana kudurinsu na yin aiki tare domin rage tashin hankalin rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da Israi'la da Amurka, tare da jaddada muhimmancin warware matsalar ta hanyar diflomasiyya.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean‑Noël Barrot, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na China, Wang Yi, inda bangarorin biyu suka amince da cewa dole ne a dauki matakan siyasa da za su dakatar da kara ruruwan rikicin tare da kare tsaron yankin gaba daya.

A cewar bayanan diflomasiyya, Faransa ta nuna damuwa kan matakan da take zargin gwamnatin Iran da dauka, ciki har da hare-hare a yankin da kuma kin bin wasu kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka shafi shirye-shiryen nukiliya da makamai masu linzami.

Kasashen biyu sun kuma jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin manyan kasashen duniya domin kauce wa kara tabarbarewar lamarin, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

Rahoton ya nuna cewa hadin gwiwar Faransa da China na daga cikin yunkurin kasashen duniya na ganin an rage tashin hankali ta hanyar diplomasiyya maimakon amfani da karfi.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form