Ƙungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun kai mummunan hari kan ƙauyen Ngoshe dake Karamar Hukumar Gwoza na Jihar Borno, yayin da mazauna garin ke ibadan azumin watan Ramadan.
Rahotanni sun bayyana cewa a wannan harin, sojoji tara da limamin ƙauyen sun rasa rayukansu, yayin da manya da yara sama da ɗari ɗaya suka shiga hannun ‘yan ta’addan.
Wadanda suka tsira sun bayyana cewa harin ya sa dubban mazauna garin barin gidajensu, inda suka tsere zuwa ƙauyuka makwabta kamar Pulka, don tsira da rayukansu. An kuma lalata gidaje da dukiyoyin jama’a da na soja.
Sanata Ali Ndume ya yi Allah wadai da wannan mummunan aiki, inda ya bukaci ƙara ƙarfin sojoji da ci gaba da ƙaddamar da ayyukan yaki da ‘yan ta’adda a yankin.
Wannan hari ya ƙara jefa al’umma cikin tashin hankali, yayin da Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kai hare-hare da yin garkuwa da mutane da kashe sojoji da fararen hula a arewa maso gabashin Najeriya.
News Translation in English Language.
Boko Haram Kills Soldiers, Abducts Women and Children in Borno.
Militants from Boko Haram/ISWAP carried out a major attack on the town of Ngoshe in Gwoza Local Government Area, Borno State, shortly after residents broke their Ramadan fast.
At least nine Nigerian soldiers and the community’s chief imam were killed during the assault, while over 100 women and children were abducted by the insurgents.
Thousands of residents reportedly fled their homes, seeking refuge in nearby communities such as Pulka, as homes and property were burned and local military positions overrun.
Senator Ali Ndume condemned the violence, calling for enhanced military capacity and sustained counter-insurgency operations in the region.
This attack adds to the ongoing Boko Haram/ISWAP insurgency in northeastern Nigeria, which continues to target both civilians and security forces through raids, killings, and kidnappings.
Tags
Labarai
_3.webp)