Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, sanannen malamin addinin Musulunci a Najeriya, ya yaba wa jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda ya bayyana cewa ya tsaya tsayin daka kan adalci.
Gumi ya ce, “Jininsa zai zama wani abin da zai motsa sauyi a cikin Al'ummah”, yana nuni da cewa wannan lamari zai hada Musulmai wajen sake samun hadin kai da karfin zuciya wajen kare hakkin al’umma.
Har ila yau, Gumi ya bayyana cewa, lokaci zai nuna sakamakon wadanda suka kasance masu hannu wajen kashe Khamenei, tare da jaddada muhimmancin kare rayukan fararen hula musamman a wuraren da rikice-rikice ke faruwa kamar Gaza.
Hukumomin Iran sun tabbatar da rasuwar Khamenei, inda aka bayyana kwanaki 40 na jimamin kasa baki daya tare da hutun kwanaki 7 ga al’umma.
Wannan lamari na daga cikin manyan abubuwan da ke iya sauya yanayin siyasa da tsaro a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
News Translation in English Language.
Gumi: Khamenei Stood for Justice, His Blood Will Inspire Change in the Ummah.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, a prominent Islamic cleric from Nigeria, has praised Iran’s Supreme Leader, Ayatollah Ali Khamenei, describing him as a steadfast advocate for justice.
Gumi said, “His blood will serve as a source of inspiration for change within the Ummah,” suggesting that this event could unite Muslims and strengthen their resolve to defend the rights of the community.
He also stated that time would reveal the consequences for those responsible for Khamenei’s death, emphasizing the importance of protecting innocent civilians in conflict zones such as Gaza.
Iranian authorities have confirmed Khamenei’s death, announcing 40 days of national mourning and a 7-day public holiday. The event is considered a significant development that could reshape political and security dynamics in the Middle East and across the globe.
Tags
Labarai
