An kammala babban bikin kamun kifi da nuna Al'adu na Argungu na shekarar 2026 cikin armashi, inda wani matashi, Abubakar Usman, ya lashe gasar kamun kifi bayan ya kamo kifi mai nauyin kilo 59.
Zakaran, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Maiyama a Jihar Kebbi, ya samu kyautar motoci biyu kirar Toyota tare da tsabar kuɗi har naira miliyan ɗaya (₦1,000,000).
Wanda ya zo na biyu, Abdullahi Garba, ya kamo kifi mai nauyin kilo 40, inda aka ba shi mota guda kirar Toyota da kuma naira miliyan ɗaya. Haka kuma, mutum biyu da suka yi kunnen doki a matsayi na uku da kifaye masu nauyin kilo 33 kowannensu, sun samu naira miliyan ɗaya da babura.
Bikin Argungu na daga cikin tsofaffin bukukuwan al’adu a Najeriya, wanda aka fara tun shekarar 1934.
Yana jawo mahalarta daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ma ƙasashen waje.
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya halarci taron, inda ya bayyana bikin a matsayin wata alama ta haɗin kai da zaman lafiya da cigaba a ƙasa.
Bikin ya ƙunshi gasar kamun kifi da kokawa da rawa da kiɗa na gargajiya tare da baje kolin sana’o’in hannu, lamarin da ke ƙarfafa yawon buɗe ido da bunƙasa tattalin arziki a jihar Kebbi.
Tags
Labarai
_2.jpeg)