Zaɓen Cike Gurbi a Kano ya Fuskanci Ƙarancin Masu Kaɗa Ƙuri’a

Zaɓen Cike Gurbi a Kano ya Fuskanci Ƙarancin Masu Kaɗa Ƙuri’a.

Zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a wasu sassan jihar Kano ya fuskanci ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a, inda rumfunan zaɓe da dama suka kasance babu cunkoso tun da safiya.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta na Ƙasa INEC sun isa rumfunan zaɓe da wuri tare da kayayyakin aiki, amma mutane kaɗan ne suka fito domin kada kuri'a.

An jibge jami’an tsaro a wurare daban-daban domin tabbatar da tsaro, yayin da wasu daga cikin ‘yan kaɗan da suka kaɗa ƙuri’a suka bayyana cewa aikin zaɓen ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.

Duk da wannan yanayi, jami’an zaɓe sun bayyana fatan cewa yawan masu kaɗa ƙuri’a zai iya ƙaruwa daga baya kafin rufe rumfunan, tare da kira ga jama’a da su fito su yi amfani da ‘yancinsu na dimokiraɗiyya domin tabbatar da sahihin wakilci a majalisar dokokin jihar.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form