Rundunar 'yan sandan Nijeriya a Jihar Neja ta ceto mutane uku da aka sace tare da kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane, biyo bayan musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga.
A cewar rundunar, an sace mutanen ne a ranar 5 ga Fabrairu, 2026, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Aworo ta hanyar Leaba Zugurma a ƙaramar hukumar Mashegu, inda suka tafi da su zuwa cikin daji.
Bayan samun bayanan sirri, jami’an ‘yan sanda daga sashen Ibbi tare da taimakon ‘yan sa-kai na yankin suka bi sahun masu garkuwar zuwa maboyarsu a cikin daji.
A safiyar ranar 8 ga Fabrairu, jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka tsere sakamakon matsin lamba, lamarin da ya bai wa ‘yan sandan damar ceto mutanen ukun lafiya lau.
A wani samame daban, rundunar ta kuma kama wani da ake zargi da fashi da makami da garkuwa da mutane, mai suna Umaru Beto, a yankin New Bussa.
An kama wanda ake zargin ne bayan wani hari a kauyen Dogon-Daji, inda aka kwato bindiga kirar gida daga hannunsa, yayin da wasu mutum biyu daga cikin ‘yan ta'addan suka tsere yayin da ake ci gaba da nemansu.
Rundunar ‘yan sanda ta ce bincike na ci gaba, tare da jaddada cewa an kara zage damtse wajen kamo sauran ‘yan bindigan da kuma kawar da dukkanin kungiyoyin da ke aikata laifuka a jihar.
Tags
Labarai
