‘Yan Sanda na neman iyaye ko dangin wannan yaron da ya bace a Jihar Adamawa.

‘Yan Sanda na neman iyaye ko dangin wannan yaron da ya bace a Jihar Adamawa.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta nemi taimakon jama’a wajen gano iyalan wani ƙaramin yaro da aka tsinta a wani wuri a Jihar.

A cewar kakakin rundunar, an tsinci yaron ne kusa da tashar NNPC Depot da ke yankin Ngurore, inda wani ɗan kirki ya kai shi ofishin ‘yan sanda na Ngurore domin kare lafiyarsa. Rundunar ta bayyana cewa yaron mai suna Yusuf Fidelis yana hannun ‘yan sanda cikin kulawa yayin da ake ci gaba da bincike don gano iyayensa ko danginsa.

‘Yan sanda sun roƙi duk wanda ke da wani bayani game da yaron ko ya san iyalansa da ya gaggauta tuntuɓar DPO na Ngurore Division domin a haɗa shi da iyalansa cikin gaggawa.

Rundunar ta jaddada muhimmancin haɗin kai daga jama’a wajen tabbatar da tsaron yara da kuma dawo da su hannun iyalansu cikin aminci.

Punchng.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form