Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyara ta yini guda zuwa jihar Kebbi a ranar Asabar domin halartar Bikin Kamun Kifi da Al'adu na Argungu.
A cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, Shugaban Ƙasar zai fara ziyarar ne da kaddamar da muhimman ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta aiwatar, kafin daga bisani ya wuce garin Argungu domin kasancewa babban bako na musamman a bikin.
Bikin Argungu na daga cikin manyan bukukuwan al’adu a Afirka, wanda ke haɗa gasa ta kamun kifi da nune-nunen al’adu da kiɗa da rawa, tare da janyo baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ƙetare.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa ziyarar Shugaban Ƙasar za ta ƙara ɗaga martabar yawon buɗe ido da al’adun jihar, tare da ba da damar ƙarfafa tattalin arziki da haɗin kan al’umma.
An kuma tabbatar da cewa an tanadi matakan tsaro da shirye-shiryen karɓar baƙi domin tabbatar da gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali da nasara.
Tags
Labarai
