Najeriya Za Ta Fara Rijistar Lambar Shaidan zama dan Ƙasa (NIN) a Matakin unguwanni Daga ranar 16 ga Fabrairu.

Najeriya Za Ta Fara Rijistar Lambar Shaidan zama dan Ƙasa (NIN) a Matakin unguwanni Daga ranar 16 ga Fabrairu.

Hukumar Samar da Katin shaidar zama dan ƙasa, (NIMC) ta sanar da cewa za ta fara rijistar Lambar Shaidan zama dan Ƙasa (NIN) a matakin unguwanni a faɗin Najeriya, daga ranar Litinin, 16 ga Fabrairu.

A cewar NIMC, shirin na da nufin kawo rijistar NIN kusa da jama’a a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni, domin sauƙaƙa wa al’umma—musamman mazauna karkara—samun damar yin rijista ba tare da wahalar tafiya mai nisa ba.

Hukumar ta bayyana cewa rijistar za ta kasance kyauta, kuma za a yi ta ne ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, tare da shugabannin gargajiya da na al’umma, domin tabbatar da isar da shirin ga kowane yanki.

NIMC ta ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya na ƙara haɗa kowa cikin tsarin shaida, tare da tallafa wa tsare-tsaren bunƙasa ƙasa da inganta gudanar da mulki a ƙarƙashin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Hukumar ta ƙara da cewa jadawalin wuraren da lokutan rijista a kowane ward za su kasance a bayyane ta hanyoyin sadarwar NIMC na hukuma, inda ta shawarci ‘yan ƙasa su bi ka’idoji tare da guje wa duk wani biyan kuɗi ga ɓata-gari, domin rijistar ba ta da kuɗi.

NIMC na sa ran cewa wannan mataki zai ƙara yawan masu rijistar NIN, tare da rage gibin rijista a yankunan da ba su da isasshen sabis, domin tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa yana da cikakkiyar shaida ta ƙasa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form