Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ba da N100 Miliyan Ga Wadanda Gobarar Kasuwar Kano Ta Shafa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ba da N100 Miliyan Ga Wadanda Gobarar Kasuwar Kano Ta Shafa.

Sanata Barau Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, ya bayar da gudummawar N100 miliyan ga 'yan kasuwar da gobarar kasuwar Singer a Unguwar Fagge, Kano ta shafa.

Gobarar ta hallaka kayayyaki da kadarori masu darajar fiye da Naira biliyan 5, inda ta shafi daruruwan 'yan kasuwa da sana’o’insu. 
Sanata Barau, wanda dan jam’iyyar APC ne kuma mai wakiltar Kano ta Arewa, ya kai ziyarar ta jajanta wa kasuwar inda ya miÆ™a gudummawarsa.

A cikin jawabi, ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan iftila'i, yana mai cewa asarar ta shafi ba kawai 'yan kasuwa ba har ma da al’umma gaba É—aya. Haka kuma, ya yi alkawarin taimakawa wajen samar da na’urar kashe gobara ta zamani a kasuwar domin kauce wa irin wannan haÉ—ari nan gaba.

Shugabannin 'yan kasuwar sun gode masa bisa wannan tallafi tare da rokon a ƙara inganta matakan tsaro da kariya a kasuwannin Kano.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form