Majalisar Tarayya zata yi Zaman Gaggawa Don Sauya Ranar Zaɓen Shugaban Ƙasa Saboda Azumin Ramadan.

Majalisar Tarayya zata yi Zaman Gaggawa Don Sauya Ranar Zaɓen Shugaban Ƙasa Saboda Azumin Ramadan.

Majalisar Tarayya ta Najeriya ta kira zaman gaggawa domin duba yiwuwar sauya ranar zaɓen Shugaban Ƙasa daga 20 ga Fabrairu zuwa 13 ga Fabrairu.

Rahoton ya bayyana cewa zaman gaggawar ya shafi Majalisar Dattawa da ta Wakilai, inda ‘yan majalisun za su tattauna batutuwan da suka shafi jadawalin zaɓe da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe.

Majiyoyi sun ce daya daga cikin manyan dalilan wannan mataki shi ne kauce wa cunkoso da matsalolin gudanar da zaɓe a lokacin azumin Ramadan, wanda ake sa ran zai fara a farkon watan Fabrairun 2027.

Haka kuma, ana sa ran majalisar za ta ba da damar doka ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) domin ta samu sassauci wajen tsara jadawalin zaɓen yadda zai bai wa ‘yan ƙasa damar kaɗa ƙuri’a cikin sauƙi.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce wannan shiri na Majalisar Tarayya na iya taimakawa wajen tabbatar da adalci, da rage ƙalubalen da ka iya tasowa a lokacin zaɓe, musamman ga masu azumi da jami’an tsaro da ma’aikatan zaɓe.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form