Kungiyoyi Tara da suka samu gurbin kaiwa zagaye na biyar na gasar FA Cup.

Kungiyoyi Tara da suka samu gurbin kaiwa zagaye na biyar na gasar FA Cup.

A kalla kungiyoyi tara zuwa yanzu sun samu gurbin shiga zagaye na biyar na FA Cup na kakar wasa ta 2025–26 bayan kammala wasannin zagaye na hudu da Suka fafata a Wannan makon.

Kungiyoyin Wrexham da Chelsea ne suka fara samun nasarar wucewa a ranar Jumma’a, yayin da wasu kungiyoyi suka bi sahunsu jiya Asabar.

A filin wasa na Etihad, Manchester City ta doke Salford 2-0, inda Rayan Ait-Nouri da Marc Guehi suka zura kwallayen.

Sai Kungiyar West Ham United ta samu wucewa bayan Crysencio Summerville ya zura kwallo daya tilo bayan karin lokaci akan Burton Albion.

A filin wasa na Villa Park, Newcastle United ce ta je har gida ta fitar da Aston Villa mai 'yan wasa 10 bayan samun jan kati, yayin da Liverpool ta tabbatar da nasarar 3-0 akan Brighton.

✅ Kungiyoyin da suka wuce zuwa zagaye na biyar:

1. Wrexham

2. Chelsea

3. Manchester City

4. West Ham United

5. Newcastle United

6. Southampton

7. Mansfield Town

8. Norwich City

9. Liverpool

Sauran Kungiyoyin zasu fafata a yau lahadi a doin cigaba da wasannin zagaye na hudu na gasar ta FA Cup.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form