Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta samu nasaran kaiwa zagaye na biyar na gasar FA Cup bayan ta doke doke Wigan da ci 4-0 a filin wasa na Emirates.
Dukkan kwallaye hudu an zura su ne a rabin lokaci na farko, cikin mintuna 27:
Noni Madueke ne ya bude wasan da cin kwallon farko a minti na 11, sannan sai
Gabriel Martinelli ya kara ta biyu a mintuna 18.
Sai Jack Hunt wanda ya yi kuskuren cin gida a mintuna 23,
Sai Gabriel Jesus Wanda ya kammala da kwallo ta hudu a minti na 27.
Wannan nasara ta tabbatar da nasaran Arsenal shiga zagaye na biyar na gasar FA Cup, karo na farko tun shekarar 2020.
Tags
Labarai
