Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sanar da korar kocinta, Thomas Frank.
An dauki wannan mataki ne bayan shan kashin da Tottenham ta yi 2-1 a gida a hannun Newcastle United a ranar Talata, sakamakon da ya bar kungiyar a matsayi na 16 a teburin Premier League, inda take da tazarar makin biyar kacal tsakaninta 'yan matakin komawa karamin gasa.
Frank dan asalin kasar Denmark ya koma Tottenham ne a bazarar bara bayan nasarorin da ya samu a Brentford, inda ya dade yana jan zarensa. Sai dai a Tottenham, abubuwa sun sauya, inda kungiyar ta shiga mawuyacin hali tare da tabarbarewar sakamako.
Tottenham ta shafe wasanni takwas na gasar Premier League a shekarar 2026 ba tare da samun nasara ko daya ba, lamarin da ya jefa Frank cikin mawuyacin hali.
Rashin nasara da ta yi a hannun Newcastle a filin wasa na Tottenham Hotspur Stadium ya zama na karshe da ya jawo korarsa. Duk da wasu alamun ci gaba a farkon aikinsa, kungiyar ta ci gaba da fama da matsaloli wajen samun nasaran wasanni.
A cikin wata sanarwa da kulob din ya wallafa a shafinsa na X, Tottenham ta ce:
“Kungiyar ta yanke shawarar yin sauyi a mukamin babban kocin kungiyar maza, kuma Thomas Frank zai bar aiki daga yau.
“An nada Thomas a watan Yunin 2025, kuma mun yi iya kokarinmu wajen ba shi lokaci da goyon bayan da ya dace domin gina makomar kungiyar. Sai dai sakamako da wasannin da ake bugawa sun sa Hukumar ta yanke cewa dole ne a yi sauyi a wannan lokaci na kakar wasa.
“Tsawon lokacinsa a kulob din, Thomas ya nuna cikakken jajircewa da sadaukarwa. Muna gode masa bisa gudunmawar da ya bayar, kuma muna masa fatan alheri a gaba.”
Tottenham na sa ran wannan sauyi zai taimaka wajen tsamo kungiyar daga halin da take ciki yayin da kakar wasa ke gab da kammalawa.
