Jami’an Tsaro Sun Yi Ƙoƙarin Kama El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Abuja.

Jami’an Tsaro Sun Yi Ƙoƙarin Kama El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Abuja.

Jami’an Tsaro Sun Yi Ƙoƙarin Kama El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Abuja.

An samu ɗan hatsaniya a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a yau Alhamis, bayan da jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, yayin da ya dawo daga birnin Cairo na ƙasar Masar.

A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, El-Rufai ya ƙi bin jami’an tsaron, yana mai jaddada cewa sai an ba shi gayyata a hukumance kafin ya amince. 
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter), Adekeye ya yi zargin cewa jami’an sun ƙwace fasfo na ƙasashen waje na El-Rufai daga hannun ɗaya daga cikin mataimakansa.

Adekeye ya rubuta cewa: “A yau jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kama Malam Nasir @elrufai yayin da ya iso daga Cairo. 
Malam El-Rufai ya ƙi bin su ba tare da gayyata a hukumance ba. Sai dai sun ƙwace fasfon dinsa na ƙasashen waje  daga hannun wani mataimakinsa.”

Har zuwa yammacin ranar Alhamis, babu wata sanarwa ta hukuma daga hukumomin tsaron najeriya da ke tabbatarwa ko musanta faruwar lamarin.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan El-Rufai ya yi wata hira da BBC Hausa, inda ya bayyana cewa zai iya fuskantar kamu a Najeriya a kowane lokaci. 
Inda ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da matsa wa ‘yan siyasa lamba, inda ya ce ana tilasta musu su bin jam’iyyar ko kuma su fuskanci matsin lamba a siyasarsu.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form