Isra’ila ta kashe mutane biyu a Gaza, ya yin da take ci gaba da hana dubban marasa lafiya ficewa neman magani ta mashigar Rafah.
A cewar rahoton Al Jazeera, wani yaro ya mutu sakamakon harin jirgin sama maras matuƙi a arewacin Gaza. Haka kuma, wani matashi mai suna Muhand Jamal al-Najjar dan (shekara 20) ya rasa ransa bayan an harbe shi a kusa da zagayen Bani Suheila a gabashin Khan Yunis.
Rahoton ya bayyana cewa Isra’ila na ci gaba da takaita ficewar marasa lafiya daga Gaza ta mashigar Rafah, duk da matsin lamba daga ƙungiyoyin jin ƙai da na lafiya. An ce kimanin mutane 260 ne kawai aka bari su ka fita domin neman magani, alhali kuwa fiye da mutane 18,500 ke cikin matsanancin buƙatar kulawar lafiya.
Ƙungiyoyin lafiya na duniya, ciki har da World Health Organization, sun yi kira da a buɗe hanyoyin fita ga marasa lafiya domin ceton rayukan fararen hula da ke fama da rauni da cututtuka masu tsanani a Gaza.
Hakan na zuwa ne a yayin da rikicin Gaza ke ci gaba, tare da ƙarin asarar rayuka da tsanantar matsalar jin ƙai a yankin.
News Translation in English Language.
Israel Kills Two in Gaza, Blocks Thousands of Patients from Exiting via Rafah.
Israeli forces have killed at least two Palestinians in separate incidents across the Gaza, while continuing to restrict the exit of thousands of patients seeking urgent medical treatment through the Rafah crossing into Egypt.
According to Al Jazeera, a child was killed in a drone strike in northern Gaza. In a separate incident, a 20-year-old Palestinian, Muhand Jamal al-Najjar, was reportedly shot dead near the Bani Suheila roundabout east of Khan Yunis.
The report states that Israeli authorities continue to severely limit medical evacuations through the Rafah crossing despite repeated appeals from humanitarian and health organisations. Only about 260 patients have been allowed to leave Gaza for treatment, even though more than 18,500 people are said to be in urgent need of specialised medical care.
International health bodies, including the World Health Organization, have called for immediate and expanded access to allow critically ill and injured civilians to receive life-saving treatment outside Gaza.
The developments come amid the ongoing conflict in Gaza, which continues to fuel a worsening humanitarian crisis and rising civilian casualties.
Tags
Labarai
