Rundunar sojin Isra’ila ta kai hari ta sama kusa da iyakar Lebanon da Syria, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane huɗu, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon da kafafen watsa labaran gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne kan wata mota a yankin gabashin Lebanon, kusa da iyakar Syria.
Harin ya faru ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Nuwamba na shekarar 2024, wadda aka tsara domin rage rikici tsakanin Isra’ila da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Lebanon, ciki har da Kungiyar Hezbollah.
A cikin bayaninta, Isra’ila ta ce harin ya nufi wasu mambobin ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad ne, wadda take da alaƙa da Hezbollah.
Sai dai hukumomin Lebanon sun bayyana cewa harin ya sake jaddada yadda ake ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da ƙara tayar da hankula a yankin.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce wannan sabon hari na nuna yadda rikici ke ci gaba da ta’azzara a arewacin Isra’ila da kudancin Lebanon, duk da ƙoƙarin ƙasashen duniya na tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan fararen hula.
Tags
Labarai
