Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta fitar da jadawalin Zaɓukan 2027, inda ta bayyana cewa zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'Yan Majalisar Ƙasa zai gudana ne a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaɓen Gwamnoni da Majalisun Jihohi zai gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja yau Juma’a, inda ya tabbatar da cewa hukumar ta shirya cikakken tsari domin gudanar da zaɓen cikin lumana da gaskiya.
Ya ce:
> “A karkashin kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 da aka yi wa gyara, wa’adin Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa da Gwamnoni da Mataimakan Gwamnonin jihohi, sai dai wasu jihohi da aka ambata, zai kare ne ranar 28 ga Mayu, 2027.
Har ila yau, membobin Majalisun Ƙasa da na Jihohi za su ƙare wa’adinsu ranar 8 ga Yuni, 2027.
A cewar sassa na 76(2), 116(2), 132(2), da 178(2) na Kundin Tsarin Mulki, zaɓen shugabannin da aka ambata ba zai gudana ba kafin kwanaki 150 kuma ba zai wuce kwanaki 30 kafin ƙarshen wa’adinsu ba.
Hukumar INEC ta bayyana cewa zaɓen zai kasance a bisa ka’ida da gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa duk matakan gudanarwa sun cika ka’ida.
Tags
Labarai
