Hare-haren ’Yan Bindiga a Pakistan Sun Hallaka ’Yan Sanda 15 da Fararen Hula 4.

Hare-haren ’Yan Bindiga a Pakistan Sun Hallaka ’Yan Sanda 15 da Fararen Hula 4.

Akalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon jerin hare-haren ’yan bindiga da suka auku a arewa maso yammacin ƙasar Pakistan a cikin kwanaki biyu, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda 15 da fararen hula hudu ne suka mutu a hare-haren da aka kai a wurare daban-daban na jihar Khyber Pakhtunkhwa, yankin da ya shahara da yawaitar hare-haren ’yan tada kayar baya. 
Haka kuma, an bayyana cewa ’yan sanda biyu sun bace bayan an yi garkuwa da su yayin wani hari.

Jami’an tsaro sun ce mafi yawan hare-haren an kai su ne ta hanyar kwanton bauna da harin bam a kan ayarin jami’an tsaro da kuma wuraren da jama’a ke taruwa. 
Ana zargin ƙungiyar Tehreek‑e‑Taliban Pakistan (TTP) da daukar alhakin wasu daga cikin hare-haren, lamarin da ke nuna karuwar ayyukan ta’addanci a yankin cikin ’yan kwanakin nan.

Gwamnati da rundunar tsaron Pakistan sun bayyana cewa sun fara tsaurara matakan tsaro tare da kaddamar da ayyukan fatattakar ’yan bindiga, domin dakile ci gaba da barazanar tsaro da kare rayukan jama’a.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa karuwar hare-haren na da alaka da matsalolin tsaro a kan iyakar Pakistan da Afghanistan, inda kungiyoyin ’yan bindiga ke cin gajiyar wahalar sarrafa yankin.

News Translation in English Language.

15 Police Officers, Four Civilians Killed in Militant Attacks in Pakistan.

Islamabad — At least 19 people have been killed in a series of militant attacks across northwestern Pakistan, security officials confirmed on Tuesday.

The casualties include 15 police personnel and four civilians, following coordinated assaults in several locations within Khyber Pakhtunkhwa province, a region long affected by insurgency and militant violence. Authorities also reported that two police officers were abducted during one of the attacks and remain missing.

According to police sources, the attacks involved ambushes and bombings targeting security patrols and civilian areas. Investigators suspect the involvement of Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), which has intensified its operations against security forces in recent months.

In response, Pakistan’s security agencies have tightened security measures and launched counter-terrorism operations aimed at tracking down those responsible and preventing further violence.

Analysts say the renewed wave of attacks highlights ongoing security challenges in Pakistan’s northwest, particularly in areas near the Afghan border, where militant groups continue to exploit difficult terrain and porous crossings.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form