Gwamnatin Taliban ta bayyana cewa a shirye take ta shiga tattaunawa da Pakistan domin rage rikicin da ke ƙara tsananta, bayan jiragen yaƙin Pakistan sun kai hare-haren sama kan manyan birane a Afghanistan, ciki har da Kabul da Kandahar.
Ministan tsaron Pakistan ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “yaƙi a fili”, yana mai cewa hare-haren na da nasaba da zargin cewa ana kai hare-hare da ake kai wa akan Pakistan daga cikin Afghanistan.
Pakistan ta jaddada cewa tana daukar matakan kare tsaron ƙasarta ne, musamman kan barazanar kungiyoyin ‘yan ta'adda.
A nata bangaren, gwamnatin Taliban ta yi Allah-wadai da hare-haren, tana mai cewa sun jawo asarar rayukan fararen hula da kuma barna ga kayayyakin more rayuwa.
Duk da haka, ta ce ƙofofin tattaunawa a bude suke domin warware sabanin ta hanyar diflomasiyya maimakon ci gaba da rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa an samu asarar rayuka da dama a bangarorin biyu, yayin da al’ummomin yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu ke fuskantar matsanancin tsoro da ƙauracewa gidajensu. Al’ummar duniya da kungiyoyin kasa da kasa sun yi kira ga bangarorin biyu da su tsagaita bude wuta tare da komawa teburin tattaunawa, domin kauce wa kara dagula zaman lafiya a yankin.
Masu sharhi na ganin cewa wannan rikici na iya zama babbar barazana ga tsaron yankin idan ba a samu mafita ta siyasa cikin gaggawa ba.
News Translation in English Language.
Taliban Signal Readiness for Talks After Pakistan Launches Airstrikes on Major Afghan Cities.
Kabul, Afghanistan — The Taliban government has said it is open to dialogue with Pakistan to de-escalate mounting tensions, following Pakistani airstrikes on major cities in Afghanistan, including Kabul and Kandahar.
Pakistan’s defence minister described the situation as an “open war,” saying the strikes were carried out in response to alleged cross-border attacks and militant threats emanating from Afghan territory. Islamabad insists the operations are defensive measures aimed at safeguarding national security.
The Taliban administration condemned the air raids, reporting civilian casualties and damage to critical infrastructure. Despite the condemnation, Taliban officials said channels for negotiation remain open, stressing a preference for diplomatic engagement over further military confrontation.
Reports indicate casualties on both sides and rising displacement among communities along the shared border, heightening fears of broader instability. International actors and regional observers have urged an immediate ceasefire and renewed dialogue to prevent a further deterioration of security.
Analysts warn that without a swift political solution, the escalation could pose a serious threat to regional peace and stability.
Tags
Labarai
