EFCC Ta Kama Mutane Uku Bisa Zargin wulakanta kudin Najeriya bayan sun share majina da Takardar naira ₦500.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta kama mutane uku bisa zargin wulakanta kudin Najeriya (Naira).
An bayyana sunayen waɗanda aka kama da Adam Muhammad, Muhammad Muhammad da Bashir Musa. An cafke su ne bayan wani bidiyo ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka gan su suna goge majina daga hancinsu da takardar kuɗi ₦500.
A cikin wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce bidiyon da ya yadu ne ya sa hukumar ta fara bincike, wanda daga bisani ya kai ga gano inda waɗanda ake zargin suke da kuma cafke su a cikin birnin Maiduguri.
Oyewale ya bayyana cewa a halin yanzu mutanen uku na tsare a cibiyar tsarewa ta EFCC da ke Maiduguri, inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
Sanarwar ta ce: “Sashen EFCC na Yankin Maiduguri ya kama mutane uku bisa zargin wulakanta Naira. Sunayen waɗanda ake zargin su ne Adam Muhammad, Muhammad Muhammad da Bashir Musa.
An kama su ne bayan wani bidiyo ya yadu a kafafen sada zumunta inda aka gan su suna goge majina daga hancinsu da takardar kuɗi ₦500.
Bayan fitar bidiyon, hukumar ta bi sawunsu tare da cafke su a cikin birnin Maiduguri.
A halin yanzu suna ƙarƙashin bincike a cibiyar tsarewa ta EFCC da ke Maiduguri, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.”
Wannan kamen na zuwa ne a daidai lokacin da EFCC ke ƙara tsaurara matakai wajen aiwatar da dokoki kan cin zarafi da wulakanta Naira.
A ‘yan makonnin nan, hukumar ta ƙara yawan kamen mutane da bincike kan waɗanda ake zargi da ɓata kuɗin ƙasa, ciki har da cafke wata fitacciyar Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, bisa zargin wulakanta Naira.
Wannan na nuna ƙoƙarin hukumar EFCC na kare martaba da mutuncin kuɗin Najeriya tare da hana ayyukan da ake ganin na tauye darajarta.
Tags
Labarai
