Dan Majalisar Wakilai daga Sokoto, Bashir Gorau, Ya Rabawa Sama da Mutane 2,000 Tallafin Karatu

Dan Majalisar Wakilai daga Sokoto, Bashir Gorau, Ya Rabawa Sama da Mutane 2,000 Tallafin Karatu

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Gada–Goronyo a Jihar Sokoto, Hon. Bashir Usman Gorau, ya raba Naira miliyan 101.4 a matsayin tallafin karatu ga sama da ɗalibai 2,000 daga mazabarsa, dake karatu a manyan makarantu daban-daban a fadin kasar nan.

Masu cin gajiyar tallafin sun hada da dalibai daga makarantun gaba da sakandare na tarayya, jihohi da masu zaman kansu, lamarin da dan majalisar ya ce shi ne ya janyo jinkirin fitar da kudaden, domin ya tabbatar da shigar kowa cikin tsari ba tare da wariya ba.

Da yake jawabi a wajen bikin rabon tallafin karatun da aka gudanar a babban dakin taro na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, Hon. Gorau ya bayyana cewa ilimi shi ne tubalin ci gaban tattalin arziki, yana mai jaddada cewa kowace kasa da ta ci gaba a duniya ta kai wannan matsayi ne ta hanyar zuba jari a harkar raya dan Adam.

 “Wannan tallafi na da manufar ci gaba da makomar mazabarmu. Duk wata tattalin arziki da kuka gani ta ci gaba a duniya, ta fara ne da gina ilimin dan Adam. 
Ba za a iya bunkasa albarkatun bil’adama ba sai ta hanyar ilimi, ingantacciyar kiwon lafiya da hanyoyin samun abin dogaro na dorewa,” in ji shi.

Hon. Gorau ya kara da cewa gwamnatinsa a majalisa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen tallafa wa matasa domin samun ilimi mai inganci da zai taimaka wajen gina al’umma mai nagarta da dogaro da kai.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form